19/09/2025
🔑 Sirrin Nasara A Rayuwar Musulmi.
🌙 TAHAJJUD + SURAH BAQARAH + ASTAGHFAR + SALAWAT = LIFE CHANGER!
Akwai wani ɗan uwa da yake cikin damuwa sosai – kuɗi babu, kwanciyar hankali babu, duk abin da ya taɓa nema yana ƙaurace masa. Duk lokacin da ya je neman shawara, sai a ce masa: “Ka yi haƙuri, rayuwa haka take.”
Sai wata rana wani malami ya ce masa:
1️⃣ Kayi Tahajjud – Sallah a tsakar dare wacce take buɗe ƙofofin rahama.
2️⃣ Surah Baqarah – Annabi ﷺ ya ce: “Kar ku bar gidajenku ba tare da karanta ta ba. Shaiɗan baya shiga gidan da aka karanta Surah Baqarah.”
3️⃣ Istighfar – Neman gafarar Allah yana kawo arziƙi da sauƙin rayuwa.
4️⃣ Salawat – Yin salati ga Annabi ﷺ yana kawo albarka da yawaitar rahama.
Ya ɗauki shawarar, ya fara yi. Ba da jimawa ba, sai ya lura da canji: zuciyarsa ta fara samun nutsuwa, damuwarsa ta ragu, Allah kuma ya fara buɗe masa ƙofofin arziki ta hanyoyi da bai taɓa zato ba.
✨ Idan kana so rayuwarka ta canza, ka fara yau:
Tahajjud
Surah Baqarah
Astaghfar
Salawat
👉 Wannan shi ne asalin life changer na Musulmi.
Copied